2 Satumba 2024 - 11:38
Falasdinawa 48 Sun Yi Shahada A Gaza / Adadin Shahidai Ya Kai 40,786

Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu a zirin Gaza ta sanar a cikin wata sanarwa a rana ta 332 na yakin cewa sojojin yahudawan sahyoniya sun sake yin kisan kiyashi har sau 3 kan fararen hula Palasdinawa a cikin sa'o'i 24 da suka gabata.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Bait (a.s) ya habarto maku bisa nakaltowa daga shafin labaraia na Quds cewa: Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu a zirin Gaza ta sanar a cikin wata sanarwa a rana ta 332 na yakin cewa sojojin yahudawan sahyoniya sun sake yin kisan kiyashi har sau 3 kan fararen hula Palasdinawa a cikin sa'o'i 24 da suka gabata.

A cikin wadannan hare-haren, Palasdinawa 48 ne suka yi shahada sannan wasu 70 suka jikkata.

Adadin shahidan yakin Gaza ya karu zuwa 40,786 kuma adadin wadanda suka jikkata ya karu zuwa 94,224 tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.

Sama da mutane 10,000 ne har yanzu ba a san su ba kuma a karkashin baraguzan gine-gine a yankuna daban-daban na zirin Gaza.